Annabi Ibrahim

6 / 25 إبراهيم Abraham Ayoyi 60

Ibrahim yana ɗaya daga cikin manyan annabawan Alƙur'ani, kuma an sa wa wata sura gabaɗaya sunansa. Labarinsa yana nuna neman gaskiya, tsayuwarsa a kan gumaka, da dogaronsa ga Allah.

2

Fasa gumaka

Ibrahim ya tambayi mutanensa menene waɗannan mutum-mutumi da suke riƙewa. Suka ce sun sami ubanninsu suna bauta musu. Ya fasa su, sai mafi girma, kuma lokacin da suka tambayi wane ne ya yi, ya ce musu su tambaye shi, idan yana iya magana. Suka ji kunya.

Nuna ayoyin (17)

۞ وَلَقَدْ ءَاتَيْنَآ إِبْرَٰهِيمَ رُشْدَهُۥ مِن قَبْلُ وَكُنَّا بِهِۦ عَٰلِمِينَ ﴿٥١﴾

Kuma lalle haƙĩƙa Mun kãwo wa Ibrãhĩm shiryuwarsa daga gabãni, kuma Mun kasance Masana gare shi.

إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِۦ مَا هَٰذِهِ ٱلتَّمَاثِيلُ ٱلَّتِىٓ أَنتُمْ لَهَا عَٰكِفُونَ ﴿٥٢﴾

Ya ce wa ubansa da mutanensa, "Mẽne ne waɗannan mutummutumai waɗanda kuke mãsu lazimta a kansu?"

قَالُوا۟ وَجَدْنَآ ءَابَآءَنَا لَهَا عَٰبِدِينَ ﴿٥٣﴾

Suka ce: "Mun sãmi Ubanninmu mãsu lazimta a kansu."

قَالَ لَقَدْ كُنتُمْ أَنتُمْ وَءَابَآؤُكُمْ فِى ضَلَٰلٍۢ مُّبِينٍۢ ﴿٥٤﴾

Ya ce: "Lalle, haƙĩƙa, kun kasance kũ da Ubanninku a cikin ɓata bayyananna."

قَالُوٓا۟ أَجِئْتَنَا بِٱلْحَقِّ أَمْ أَنتَ مِنَ ٱللَّٰعِبِينَ ﴿٥٥﴾

Suka ce: "Shin kã zo mana da gaskiya ne, Kõ kuwa kai kanã daga mãSu wãsã ne?"

قَالَ بَل رَّبُّكُمْ رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ٱلَّذِى فَطَرَهُنَّ وَأَنَا۠ عَلَىٰ ذَٰلِكُم مِّنَ ٱلشَّٰهِدِينَ ﴿٥٦﴾

Ya ce: "Ã'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka."

وَتَٱللَّهِ لَأَكِيدَنَّ أَصْنَٰمَكُم بَعْدَ أَن تُوَلُّوا۟ مُدْبِرِينَ ﴿٥٧﴾

"Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya."

فَجَعَلَهُمْ جُذَٰذًا إِلَّا كَبِيرًۭا لَّهُمْ لَعَلَّهُمْ إِلَيْهِ يَرْجِعُونَ ﴿٥٨﴾

Sai ya sanya su guntu-guntu fãce wani babba gare su, tsammãninsũ sunã Kõmãwa zuwa gare shi.

قَالُوا۟ مَن فَعَلَ هَٰذَا بِـَٔالِهَتِنَآ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ ﴿٥٩﴾

Suka ce: "Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu? Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga azzãlumai."

قَالُوا۟ سَمِعْنَا فَتًۭى يَذْكُرُهُمْ يُقَالُ لَهُۥٓ إِبْرَٰهِيمُ ﴿٦٠﴾

Suka ce: "Mun ji wani saurayi yanã ambatar su. Anã ce masa Ibrahĩm."

قَالُوا۟ فَأْتُوا۟ بِهِۦ عَلَىٰٓ أَعْيُنِ ٱلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَشْهَدُونَ ﴿٦١﴾

Suka ce: "To, ku zo da shi a kan idanun mutãne, tsammãnin su zã su bãyar da shaida."

قَالُوٓا۟ ءَأَنتَ فَعَلْتَ هَٰذَا بِـَٔالِهَتِنَا يَٰٓإِبْرَٰهِيمُ ﴿٦٢﴾

Suka ce: "Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm!"

قَالَ بَلْ فَعَلَهُۥ كَبِيرُهُمْ هَٰذَا فَسْـَٔلُوهُمْ إِن كَانُوا۟ يَنطِقُونَ ﴿٦٣﴾

Ya ce: "Ã'a, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana."

فَرَجَعُوٓا۟ إِلَىٰٓ أَنفُسِهِمْ فَقَالُوٓا۟ إِنَّكُمْ أَنتُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ ﴿٦٤﴾

Sai suka kõma wa jũnansu suka ce: "Lalle ne kũ, kũ ne azzãlumai."

ثُمَّ نُكِسُوا۟ عَلَىٰ رُءُوسِهِمْ لَقَدْ عَلِمْتَ مَا هَٰٓؤُلَآءِ يَنطِقُونَ ﴿٦٥﴾

Sa'an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kãwunansu (sukace,) "Lalle, haƙĩƙa, kã sani waɗannan bã su yin magana."

قَالَ أَفَتَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكُمْ شَيْـًۭٔا وَلَا يَضُرُّكُمْ ﴿٦٦﴾

Ya ce: "Shin to, kunã bautã wa abin da, bã ya, amfãnin ku da Kõme kuma bã ya cũtar da ku baicin Allah?"

أُفٍّۢ لَّكُمْ وَلِمَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ ۖ أَفَلَا تَعْقِلُونَ ﴿٦٧﴾

"Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, baicin Allah! Shin to, bã ku hankalta?"

3

Wutar

Mutanensa suka ce a ƙone shi. Allah ya ce wa wutar ta zama sanyi da aminci ga Ibrahim, kuma su ne manyan hasararru. Ibrahim ya ce yana ƙaura zuwa ga Ubangijinsa, kuma Allah ya ba shi Ishaq da Yaƙubu.

Nuna ayoyin (7)

قَالُوا۟ حَرِّقُوهُ وَٱنصُرُوٓا۟ ءَالِهَتَكُمْ إِن كُنتُمْ فَٰعِلِينَ ﴿٦٨﴾

Suka ce: "Ku ƙõne shi kuma ku taimaki gumãkanku, idan kun kasance mãsu aikatãwa."

قُلْنَا يَٰنَارُ كُونِى بَرْدًۭا وَسَلَٰمًا عَلَىٰٓ إِبْرَٰهِيمَ ﴿٦٩﴾

Muka ce: "Yã wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm."

وَأَرَادُوا۟ بِهِۦ كَيْدًۭا فَجَعَلْنَٰهُمُ ٱلْأَخْسَرِينَ ﴿٧٠﴾

Kuma suka yi nufin wani mũgun shiri da shi, sai Mukasanya su mafiya hasãra.

فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِۦٓ إِلَّآ أَن قَالُوا۟ ٱقْتُلُوهُ أَوْ حَرِّقُوهُ فَأَنجَىٰهُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلنَّارِ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَءَايَٰتٍۢ لِّقَوْمٍۢ يُؤْمِنُونَ ﴿٢٤﴾

Sa'an nan bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa (Ibrãhĩm) fãce dai suka ce: "Ku kashe shi kõ, ku ƙõnã shi," Sai Allah Ya tsĩrar da shi daga wutã. Lallea cikin wannan akwai ayõyi ga mutãnen da ke yin ĩmãni.

وَقَالَ إِنَّمَا ٱتَّخَذْتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ أَوْثَٰنًۭا مَّوَدَّةَ بَيْنِكُمْ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ۖ ثُمَّ يَوْمَ ٱلْقِيَٰمَةِ يَكْفُرُ بَعْضُكُم بِبَعْضٍۢ وَيَلْعَنُ بَعْضُكُم بَعْضًۭا وَمَأْوَىٰكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّٰصِرِينَ ﴿٢٥﴾

Kuma Ibrahĩm ya ce "Bãbu abin da kuka yi sai dai kub bar Allah kun riƙi gumãka sabõda sõyayyar tsakãninku a cikin rãyuwar dũniya, a'an nan a Rãnar ¡iyãma sãshinku zai kãfirce wa sãshi, kuma makõmarku ita ce wutã kuma bã ku da waɗansu mataimaka."

۞ فَـَٔامَنَ لَهُۥ لُوطٌۭ ۘ وَقَالَ إِنِّى مُهَاجِرٌ إِلَىٰ رَبِّىٓ ۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ ﴿٢٦﴾

Sai Lũɗu ya yi ĩmãni da shi. Kuma Ibrãhĩm ya ce: "Lallenĩ mai ƙaura ne zuwa ga Ubangijina. Lalle Shĩ Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima."

وَوَهَبْنَا لَهُۥٓ إِسْحَٰقَ وَيَعْقُوبَ وَجَعَلْنَا فِى ذُرِّيَّتِهِ ٱلنُّبُوَّةَ وَٱلْكِتَٰبَ وَءَاتَيْنَٰهُ أَجْرَهُۥ فِى ٱلدُّنْيَا ۖ وَإِنَّهُۥ فِى ٱلْءَاخِرَةِ لَمِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ ﴿٢٧﴾

Kuma Muka bã shi Ishãƙa da Ya'aƙũba, kuma Muka sanya Annabci da littãfi a cikin zuriyarsa. Kuma Mun bã shi sakamakonsa a dũniya, kuma lalle shĩ a Lãhira, tabbas, yanã a cikin sãlihai.

4

Ɗakin

Ibrahim da Isma'il suka ɗaga harsashin Ɗakin kuma suka yi addu'a Allah ya karɓa daga gare su. Ibrahim ya roƙi Allah da ya sanya birnin ya zama amintacce, ya arzurta mutanensa, kuma ya aiko musu da manzo daga cikinsu.

Nuna ayoyin (12)

وَإِذْ جَعَلْنَا ٱلْبَيْتَ مَثَابَةًۭ لِّلنَّاسِ وَأَمْنًۭا وَٱتَّخِذُوا۟ مِن مَّقَامِ إِبْرَٰهِۦمَ مُصَلًّۭى ۖ وَعَهِدْنَآ إِلَىٰٓ إِبْرَٰهِۦمَ وَإِسْمَٰعِيلَ أَن طَهِّرَا بَيْتِىَ لِلطَّآئِفِينَ وَٱلْعَٰكِفِينَ وَٱلرُّكَّعِ ٱلسُّجُودِ ﴿١٢٥﴾

Kuma a lõkacin da Muka sanya ¦ãkin ya zama makõma ga mutãne, da aminci, kuma ku riƙi wurin salla daga Maƙãmi Ibrãhĩm, kuma Muka yi alƙawari zuwa ga Ibrãhĩm, da Ismã'ila da cẽwa: "Ku tsarkake ¦ãkiNa dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu lizimta da mãsu rukũ'i, mãsu sujada."

وَإِذْ قَالَ إِبْرَٰهِۦمُ رَبِّ ٱجْعَلْ هَٰذَا بَلَدًا ءَامِنًۭا وَٱرْزُقْ أَهْلَهُۥ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ مَنْ ءَامَنَ مِنْهُم بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْءَاخِرِ ۖ قَالَ وَمَن كَفَرَ فَأُمَتِّعُهُۥ قَلِيلًۭا ثُمَّ أَضْطَرُّهُۥٓ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلنَّارِ ۖ وَبِئْسَ ٱلْمَصِيرُ ﴿١٢٦﴾

Kuma a lõkacin da lbrãhĩm ya ce: "Yã Ubangijĩna! Ka sanya wannan gari amintacce, Ka azurta mutãnensa, daga 'ya'yan itãcen, wanda ya yi ĩmãni, daga gare su, da Allah da Ranar Lãhira." Allah Ya ce: "Wanda ya kãfirta ma Ina jiyar da shi dãɗi kaɗan, sa'an nan kuma Ina tĩlastã shi zuwa ga azãbar Wuta. Kuma makõmar, ta munana."

وَإِذْ يَرْفَعُ إِبْرَٰهِۦمُ ٱلْقَوَاعِدَ مِنَ ٱلْبَيْتِ وَإِسْمَٰعِيلُ رَبَّنَا تَقَبَّلْ مِنَّآ ۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ ﴿١٢٧﴾

Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm yake ɗaukaka harsãshin gini ga ¦ãkin, da Ismã'ĩla (suna cẽwa:) "Yã Ubangijnmu! Ka karɓa daga gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Mai sani.

رَبَّنَا وَٱجْعَلْنَا مُسْلِمَيْنِ لَكَ وَمِن ذُرِّيَّتِنَآ أُمَّةًۭ مُّسْلِمَةًۭ لَّكَ وَأَرِنَا مَنَاسِكَنَا وَتُبْ عَلَيْنَآ ۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ ﴿١٢٨﴾

"Ya Ubangijnmu! Ka sanyã mu, mu biyu, waɗanda suka sallama (al'amari) gare Ka, kuma daga zuriyarmu (Ka sanya) al'umma mai sallamãwa zuwa gare Ka, Kuma Ka nũna mana wurãren ibãdar hajjinmu, kuma Ka karɓi tũba a kanmu. Lalle ne Kai, Kai ne Mai karɓar tũba, Mai rahama.

رَبَّنَا وَٱبْعَثْ فِيهِمْ رَسُولًۭا مِّنْهُمْ يَتْلُوا۟ عَلَيْهِمْ ءَايَٰتِكَ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلْكِتَٰبَ وَٱلْحِكْمَةَ وَيُزَكِّيهِمْ ۚ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ ﴿١٢٩﴾

"Ya Ubangijinmu! Ka aiko, a cikinsu, wani manzo daga gare su, yana karanta musu ãyõyinKa, kuma yana karantar da su Littãfin da hikimar, kuma yana tsarkake su. Lalle ne Kai, Kai ne Mabuwãyi Mai hikima."

وَإِذْ قَالَ إِبْرَٰهِيمُ رَبِّ ٱجْعَلْ هَٰذَا ٱلْبَلَدَ ءَامِنًۭا وَٱجْنُبْنِى وَبَنِىَّ أَن نَّعْبُدَ ٱلْأَصْنَامَ ﴿٣٥﴾

Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanyã wannan gari amintacce kuma Ka nĩsanta ni, nĩ da ɗiyãna daga bauta wa gumãka.

رَبِّ إِنَّهُنَّ أَضْلَلْنَ كَثِيرًۭا مِّنَ ٱلنَّاسِ ۖ فَمَن تَبِعَنِى فَإِنَّهُۥ مِنِّى ۖ وَمَنْ عَصَانِى فَإِنَّكَ غَفُورٌۭ رَّحِيمٌۭ ﴿٣٦﴾

"Yã Ubangijina! Lalle ne sũ, sun ɓatar da mãsu yawa daga mutãne sa'an nan wanda ya bĩ ni, to, lalle shi, yanã daga gare ni, kuma wanda ya sãɓa mini, to, lalle ne Kai Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

رَّبَّنَآ إِنِّىٓ أَسْكَنتُ مِن ذُرِّيَّتِى بِوَادٍ غَيْرِ ذِى زَرْعٍ عِندَ بَيْتِكَ ٱلْمُحَرَّمِ رَبَّنَا لِيُقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ فَٱجْعَلْ أَفْـِٔدَةًۭ مِّنَ ٱلنَّاسِ تَهْوِىٓ إِلَيْهِمْ وَٱرْزُقْهُم مِّنَ ٱلثَّمَرَٰتِ لَعَلَّهُمْ يَشْكُرُونَ ﴿٣٧﴾

"Yã Ubangijinmu! Lalle ne ni, na zaunar da zuriyata ga rãfi wanda ba ma'abũcin shũka ba, a wurin ¦ãkinka mai alfarma. Yã Ubangijinmu! Dõmin su tsayar da salla. Sai Ka sanya zukãta daga mutãne sunã gaggãwar bẽgenzuwa gare su, kuma ka azurtã su daga 'ya'yan itãce, mai yiwuwã ne sunã gõdẽwã."

رَبَّنَآ إِنَّكَ تَعْلَمُ مَا نُخْفِى وَمَا نُعْلِنُ ۗ وَمَا يَخْفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِن شَىْءٍۢ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا فِى ٱلسَّمَآءِ ﴿٣٨﴾

"Yã Ubangijinmu! Lalle ne Kai Kanã sanin abin da muke ɓõyẽwa, da abin da muke bayyanãwa. Kuma bãbu abin da yake ɓõyẽwa ga A1lah, daga wani abu a cikin ƙasa, kuma bãbu a cikin sama."

ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ ٱلَّذِى وَهَبَ لِى عَلَى ٱلْكِبَرِ إِسْمَٰعِيلَ وَإِسْحَٰقَ ۚ إِنَّ رَبِّى لَسَمِيعُ ٱلدُّعَآءِ ﴿٣٩﴾

"Gõdiyã ta tabbata ga Allah wanda Yake Ya bã ni inã a cikin tsufa Ismã'ila da Is'hãƙa. Lalle ne Ubangijina, haƙĩƙa, Mai jin addu'a ne."

رَبِّ ٱجْعَلْنِى مُقِيمَ ٱلصَّلَوٰةِ وَمِن ذُرِّيَّتِى ۚ رَبَّنَا وَتَقَبَّلْ دُعَآءِ ﴿٤٠﴾

"Yã Ubangijina! Ka sanyã ni mai tsayar da salla. Kuma daga zũriyyata. Yã Ubangijinmu! Kuma Ka karɓi addu'ata."

رَبَّنَا ٱغْفِرْ لِى وَلِوَٰلِدَىَّ وَلِلْمُؤْمِنِينَ يَوْمَ يَقُومُ ٱلْحِسَابُ ﴿٤١﴾

"Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara gare ni, kuma ga mahaifãna, kuma da mũminai, a rãnar da hisãbi yake tsayãwa."

5

Babban gwaji

An ba Ibrahim bishara ta ɗa mai haƙuri. Lokacin da yaron ya iya aiki tare da shi, Ibrahim ya ce ya ga a mafarki yana yanka shi. Ɗan ya ce masa ya yi abin da aka umarce shi kuma zai yi haƙuri. Lokacin da duka biyun suka miƙa wuya, Allah ya kira Ibrahim kuma ya fanshi yaron da babbar hadaya. Alƙur'ani bai ambaci sunan ɗan a wannan wuri ba, kuma malamai sun yi savani kan wane ne shi.

Nuna ayoyin (13)

وَقَالَ إِنِّى ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّى سَيَهْدِينِ ﴿٩٩﴾

Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."

رَبِّ هَبْ لِى مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ ﴿١٠٠﴾

"Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."

فَبَشَّرْنَٰهُ بِغُلَٰمٍ حَلِيمٍۢ ﴿١٠١﴾

Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.

فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ ٱلسَّعْىَ قَالَ يَٰبُنَىَّ إِنِّىٓ أَرَىٰ فِى ٱلْمَنَامِ أَنِّىٓ أَذْبَحُكَ فَٱنظُرْ مَاذَا تَرَىٰ ۚ قَالَ يَٰٓأَبَتِ ٱفْعَلْ مَا تُؤْمَرُ ۖ سَتَجِدُنِىٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّٰبِرِينَ ﴿١٠٢﴾

To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."

فَلَمَّآ أَسْلَمَا وَتَلَّهُۥ لِلْجَبِينِ ﴿١٠٣﴾

To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa.

وَنَٰدَيْنَٰهُ أَن يَٰٓإِبْرَٰهِيمُ ﴿١٠٤﴾

Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!"

قَدْ صَدَّقْتَ ٱلرُّءْيَآ ۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ ﴿١٠٥﴾

"Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلْبَلَٰٓؤُا۟ ٱلْمُبِينُ ﴿١٠٦﴾

Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.

وَفَدَيْنَٰهُ بِذِبْحٍ عَظِيمٍۢ ﴿١٠٧﴾

Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.

وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِى ٱلْءَاخِرِينَ ﴿١٠٨﴾

Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.

سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِبْرَٰهِيمَ ﴿١٠٩﴾

Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.

كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ ﴿١١٠﴾

Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

إِنَّهُۥ مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ ﴿١١١﴾

Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.

6

Baƙi masu bishara

Manzanni sun zo wurin Ibrahim da gaisuwar aminci, kuma ya kawo musu ɗan maraƙi gasasshe. Lokacin da hannayensu ba su miƙa zuwa gare shi ba, ya ji tsoro. Suka ce masa kada ya ji tsoro, cewa an aiko su zuwa ga mutanen Lutu, kuma suka ba matarsa bishara ta Ishaq, kuma bayansa, Yaƙubu.

Nuna ayoyin (5)

وَلَقَدْ جَآءَتْ رُسُلُنَآ إِبْرَٰهِيمَ بِٱلْبُشْرَىٰ قَالُوا۟ سَلَٰمًۭا ۖ قَالَ سَلَٰمٌۭ ۖ فَمَا لَبِثَ أَن جَآءَ بِعِجْلٍ حَنِيذٍۢ ﴿٦٩﴾

Kuma haƙĩƙa, manzanninMu sun je wa Ibrãhim da bushãra suka ce: "Aminci." Ya ce: "Aminci (ya tabbata a gare ku)." Sa'an nan bai yi jinkiri ba ya je da maraƙi ƙawãtacce.

فَلَمَّا رَءَآ أَيْدِيَهُمْ لَا تَصِلُ إِلَيْهِ نَكِرَهُمْ وَأَوْجَسَ مِنْهُمْ خِيفَةًۭ ۚ قَالُوا۟ لَا تَخَفْ إِنَّآ أُرْسِلْنَآ إِلَىٰ قَوْمِ لُوطٍۢ ﴿٧٠﴾

Sa'an nan a lõkacin da ya ga hannayensu bã su sãduwa zuwa gare shi (maraƙin), sai ya yi ƙyãmarsu, kuma ya ji tsõronsu. Suka ce, "Kada kaji tsõro lalle ne mũ, an aiko mu ne zuwa ga mutãnen Lũɗu"

وَٱمْرَأَتُهُۥ قَآئِمَةٌۭ فَضَحِكَتْ فَبَشَّرْنَٰهَا بِإِسْحَٰقَ وَمِن وَرَآءِ إِسْحَٰقَ يَعْقُوبَ ﴿٧١﴾

Kuma mãtarsa tanã tsaye. Ta yi dãriya. Sai Muka yi mata bushãra (da haihuwar) Is'hãƙa, kuma a bayan Is'hãƙa, Yãƙũbu.

قَالَتْ يَٰوَيْلَتَىٰٓ ءَأَلِدُ وَأَنَا۠ عَجُوزٌۭ وَهَٰذَا بَعْلِى شَيْخًا ۖ إِنَّ هَٰذَا لَشَىْءٌ عَجِيبٌۭ ﴿٧٢﴾

Sai ta ce: "Yã kaitõna! Shin, zan haihu ne alhãli kuwa inã tsõhuwa, kuma ga mijĩna tsõho ne? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmãki."

قَالُوٓا۟ أَتَعْجَبِينَ مِنْ أَمْرِ ٱللَّهِ ۖ رَحْمَتُ ٱللَّهِ وَبَرَكَٰتُهُۥ عَلَيْكُمْ أَهْلَ ٱلْبَيْتِ ۚ إِنَّهُۥ حَمِيدٌۭ مَّجِيدٌۭ ﴿٧٣﴾

Suka ce: "Shin kinã mãmaki ne daga al'amarin Allah? Rahamar Allah da albarkarSa su tabbata a kanku, ya mutãnen babban gida! Lalle ne Shĩ abin gõdewa ne, Mai girma."

An ɗauko wannan labari daga Alƙur'ani kaɗai. Ba a ƙara bayanai daga wasu littattafai ba.

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi.

Tambayoyi game da annabawa

Wane ne Annabi Ibrahim?

Ibrahim yana ɗaya daga cikin manyan annabawan Alƙur'ani, kuma an sa wa wata sura gabaɗaya sunansa. Labarinsa yana nuna neman gaskiya, tsayuwarsa a kan gumaka, da dogaronsa ga Allah.

Ina labarin Ibrahim yake a Alƙur'ani?

Yana cikin Al-An'am 6:74–79, Al-Anbiya 21:51–67, Al-Anbiya 21:68–70, Al-'Ankabut 29:24–27, Al-Baqarah 2:125–129, Ibrahim 14:35–41, As-Saffat 37:99–111, Hud 11:69–73. Wannan shafi yana nuna waɗannan ayoyi da Larabci da kuma harshenka.

This page is translated with machine assistance and may contain mistakes. The English and Arabic versions are our reference. About our sources