Mai gaskiya a alƙawari
Allah ya ce Isma'il mai gaskiya ne a alƙawari, manzo kuma annabi. Ya umarci iyalinsa da yin sallah da ba da zakka, kuma ya kasance abin yardar Ubangijinsa.
Nuna ayoyin (2)
وَٱذْكُرْ فِى ٱلْكِتَٰبِ إِسْمَٰعِيلَ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ صَادِقَ ٱلْوَعْدِ وَكَانَ رَسُولًۭا نَّبِيًّۭا ﴿٥٤﴾
Kuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi.
وَكَانَ يَأْمُرُ أَهْلَهُۥ بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ وَكَانَ عِندَ رَبِّهِۦ مَرْضِيًّۭا ﴿٥٥﴾
Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnens da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa.