Sura ta 83 a Alƙur'ani

Sura Al-Mutaffifin

Makkiyya Aya 36 Juzu'i 30
Al-Mutaffifin

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَيْلٌۭ لِّلْمُطَفِّفِينَ ﴿١﴾

Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

ٱلَّذِينَ إِذَا ٱكْتَالُوا۟ عَلَى ٱلنَّاسِ يَسْتَوْفُونَ ﴿٢﴾

Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَإِذَا كَالُوهُمْ أَو وَّزَنُوهُمْ يُخْسِرُونَ ﴿٣﴾

Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

أَلَا يَظُنُّ أُو۟لَٰٓئِكَ أَنَّهُم مَّبْعُوثُونَ ﴿٤﴾

Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

لِيَوْمٍ عَظِيمٍۢ ﴿٥﴾

Domin yini mai girma.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

يَوْمَ يَقُومُ ٱلنَّاسُ لِرَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ ﴿٦﴾

Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلْفُجَّارِ لَفِى سِجِّينٍۢ ﴿٧﴾

Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا سِجِّينٌۭ ﴿٨﴾

Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

كِتَٰبٌۭ مَّرْقُومٌۭ ﴿٩﴾

Wani 1ittãfi ne rubũtacce.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَيْلٌۭ يَوْمَئِذٍۢ لِّلْمُكَذِّبِينَ ﴿١٠﴾

Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

ٱلَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوْمِ ٱلدِّينِ ﴿١١﴾

Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَمَا يُكَذِّبُ بِهِۦٓ إِلَّا كُلُّ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ ﴿١٢﴾

Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ ءَايَٰتُنَا قَالَ أَسَٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ ﴿١٣﴾

Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

كَلَّا ۖ بَلْ ۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ ﴿١٤﴾

A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

كَلَّآ إِنَّهُمْ عَن رَّبِّهِمْ يَوْمَئِذٍۢ لَّمَحْجُوبُونَ ﴿١٥﴾

A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُوا۟ ٱلْجَحِيمِ ﴿١٦﴾

Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

ثُمَّ يُقَالُ هَٰذَا ٱلَّذِى كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ ﴿١٧﴾

Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلْأَبْرَارِ لَفِى عِلِّيِّينَ ﴿١٨﴾

A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا عِلِّيُّونَ ﴿١٩﴾

Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

كِتَٰبٌۭ مَّرْقُومٌۭ ﴿٢٠﴾

Wani littãfi ne rubũtacce.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

يَشْهَدُهُ ٱلْمُقَرَّبُونَ ﴿٢١﴾

Muƙarrabai suke halarta shi.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

إِنَّ ٱلْأَبْرَارَ لَفِى نَعِيمٍ ﴿٢٢﴾

Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

عَلَى ٱلْأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ ﴿٢٣﴾

A kan karagu, suna ta kallo.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

تَعْرِفُ فِى وُجُوهِهِمْ نَضْرَةَ ٱلنَّعِيمِ ﴿٢٤﴾

Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

يُسْقَوْنَ مِن رَّحِيقٍۢ مَّخْتُومٍ ﴿٢٥﴾

Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

خِتَٰمُهُۥ مِسْكٌۭ ۚ وَفِى ذَٰلِكَ فَلْيَتَنَافَسِ ٱلْمُتَنَٰفِسُونَ ﴿٢٦﴾

¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَمِزَاجُهُۥ مِن تَسْنِيمٍ ﴿٢٧﴾

Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

عَيْنًۭا يَشْرَبُ بِهَا ٱلْمُقَرَّبُونَ ﴿٢٨﴾

(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

إِنَّ ٱلَّذِينَ أَجْرَمُوا۟ كَانُوا۟ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ يَضْحَكُونَ ﴿٢٩﴾

Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَإِذَا مَرُّوا۟ بِهِمْ يَتَغَامَزُونَ ﴿٣٠﴾

Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَإِذَا ٱنقَلَبُوٓا۟ إِلَىٰٓ أَهْلِهِمُ ٱنقَلَبُوا۟ فَكِهِينَ ﴿٣١﴾

Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوٓا۟ إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ لَضَآلُّونَ ﴿٣٢﴾

Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَمَآ أُرْسِلُوا۟ عَلَيْهِمْ حَٰفِظِينَ ﴿٣٣﴾

Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

فَٱلْيَوْمَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مِنَ ٱلْكُفَّارِ يَضْحَكُونَ ﴿٣٤﴾

To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

عَلَى ٱلْأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ ﴿٣٥﴾

A kan karagu, suna ta kallo.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

هَلْ ثُوِّبَ ٱلْكُفَّارُ مَا كَانُوا۟ يَفْعَلُونَ ﴿٣٦﴾

Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

Al-Mutaffifin Aya 1 cikin 36

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura Al-Mutaffifin

Sura Al-Mutaffifin (المطففين) ita ce sura ta 83 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 36 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, المطففين, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura Al-Mutaffifin

Ayoyi nawa ne a Sura Al-Mutaffifin?

Sura Al-Mutaffifin tana da ayoyi 36.

Shin Sura Al-Mutaffifin ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura Al-Mutaffifin take?

Sura Al-Mutaffifin tana Juzu'i na 30.

A ina zan saurari Sura Al-Mutaffifin?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Abdur-Rahman As-Sudais, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

This page is translated with machine assistance and may contain mistakes. The English and Arabic versions are our reference. About our sources