Jirgin ruwa da kifin
Yunusa ya gudu zuwa jirgin ruwa mai nauyi. Suka jefa kuri'a kuma yana cikin waɗanda suka yi rashin nasara, kuma kifin ya haɗiye shi yayin da yake abin zargi. Da ba don yana cikin masu tsarkake Allah ba, da ya zauna a cikinsa har zuwa Ranar da za a tashe su. An jefa shi a gaɓar da ba ciyayi, yana rashin lafiya, kuma wata ƙwarya ta tsiro a kansa.
Nuna ayoyin (10)
وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ ﴿١٣٩﴾
Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
إِذْ أَبَقَ إِلَى ٱلْفُلْكِ ٱلْمَشْحُونِ ﴿١٤٠﴾
A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.
فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ ٱلْمُدْحَضِينَ ﴿١٤١﴾
Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.
فَٱلْتَقَمَهُ ٱلْحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٌۭ ﴿١٤٢﴾
Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
فَلَوْلَآ أَنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلْمُسَبِّحِينَ ﴿١٤٣﴾
To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,
لَلَبِثَ فِى بَطْنِهِۦٓ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ ﴿١٤٤﴾
Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.
۞ فَنَبَذْنَٰهُ بِٱلْعَرَآءِ وَهُوَ سَقِيمٌۭ ﴿١٤٥﴾
Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.
وَأَنۢبَتْنَا عَلَيْهِ شَجَرَةًۭ مِّن يَقْطِينٍۢ ﴿١٤٦﴾
Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.
وَأَرْسَلْنَٰهُ إِلَىٰ مِا۟ئَةِ أَلْفٍ أَوْ يَزِيدُونَ ﴿١٤٧﴾
Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).
فَـَٔامَنُوا۟ فَمَتَّعْنَٰهُمْ إِلَىٰ حِينٍۢ ﴿١٤٨﴾
Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.