Sura ta 91 a Alƙur'ani

Sura Ash-Shams

Makkiyya Aya 15 Juzu'i 30
Ash-Shams

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلشَّمْسِ وَضُحَىٰهَا ﴿١﴾

Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَٱلْقَمَرِ إِذَا تَلَىٰهَا ﴿٢﴾

Kuma da wata idan ya bi ta.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَٱلنَّهَارِ إِذَا جَلَّىٰهَا ﴿٣﴾

Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَٱلَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰهَا ﴿٤﴾

Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَٱلسَّمَآءِ وَمَا بَنَىٰهَا ﴿٥﴾

Da sama da abin da ya gina ta.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَٱلْأَرْضِ وَمَا طَحَىٰهَا ﴿٦﴾

Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَنَفْسٍۢ وَمَا سَوَّىٰهَا ﴿٧﴾

Da rai da abin da ya daidaita shi.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَىٰهَا ﴿٨﴾

Sa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّىٰهَا ﴿٩﴾

Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَقَدْ خَابَ مَن دَسَّىٰهَا ﴿١٠﴾

Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِطَغْوَىٰهَآ ﴿١١﴾

Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

إِذِ ٱنۢبَعَثَ أَشْقَىٰهَا ﴿١٢﴾

A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ ٱللَّهِ نَاقَةَ ٱللَّهِ وَسُقْيَٰهَا ﴿١٣﴾

Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمْدَمَ عَلَيْهِمْ رَبُّهُم بِذَنۢبِهِمْ فَسَوَّىٰهَا ﴿١٤﴾

Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَلَا يَخَافُ عُقْبَٰهَا ﴿١٥﴾

Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

Ash-Shams Aya 1 cikin 15

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura Ash-Shams

Sura Ash-Shams (الشمس) ita ce sura ta 91 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 15 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, الشمس, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura Ash-Shams

Ayoyi nawa ne a Sura Ash-Shams?

Sura Ash-Shams tana da ayoyi 15.

Shin Sura Ash-Shams ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura Ash-Shams take?

Sura Ash-Shams tana Juzu'i na 30.

A ina zan saurari Sura Ash-Shams?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Abdur-Rahman As-Sudais, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

This page is translated with machine assistance and may contain mistakes. The English and Arabic versions are our reference. About our sources