Abin da za a faɗa bayan kammala sallah
((أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ (ثَلاَثَاً) اللَّهُمَّ أَنْتَ السَّلاَمُ، وَمِنْكَ السَّلاَمُ، تَبَارَكْتَ يَا ذَا الْجَلاَلِ وَالْإِكْرَامِ)).
(Ina neman gafarar Allah.(sau uku) (Ya Allah, Kai ne As-Salam, kuma daga gare Ka ne dukkan aminci yake, Ka yi albarka, ya Ma’abucin girma da karamci.) (AS-Salam: Wanda Yake nesa da dukkan aibi da naƙasa.))
((لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ [ثلاثاً]، اللَّهُمَّ لاَ مَانِعَ لِمَا أَعْطَيْتَ، وَلاَ مُعْطِيَ لِمَا مَنَعْتَ، وَلاَ يَنْفَعُ ذَا الْجَدِّ مِنْكَ الجَدُّ)).
(Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne kuma godiya tasa ce, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan komai.Ya Allah, babu mai hana abin da Ka yi nufin bayarwa, kuma babu mai bayar da abin da Ka yi nufin hanawa, kuma dukiya ko ɗaukaka ba ta amfanar da kowa, domin daga gare Ka ne dukiya da ɗaukaka suke.)
((لَا إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ. لاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَلاَ نَعْبُدُ إِلاَّ إِيَّاهُ, لَهُ النِّعْمَةُ وَلَهُ الْفَضْلُ وَلَهُ الثَّنَاءُ الْحَسَنُ، لَا إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الكَافِرُونَ)).
(Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne kuma godiya tasa ce, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan komai. Babu dabara babu ƙarfi sai da Allah, babu abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma ba ma bauta wa kowa sai Shi. Gare Shi ne ni’ima take, da falala, da kyakkyawar yabo mai ɗaukaka. Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma muna tsarkake addini gare Shi, ko da kafirai sun ƙi.)
((سُبْحَانَ اللَّهِ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، وَاللَّهُ أَكْبَرُ (ثلاثاً وثلاثين) لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ)).
(Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, kuma Allah ne Mafi girma.(sau talatin da uku) (Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne kuma godiya tasa ce, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan komai.))
بسم الله الرحمن الرحيم ﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ اللَّهُ الصَّمَدُ لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ وَلَمْ يَكُن لَّهُ كُفُواً أَحَدٌ﴾، بسم الله الرحمن الرحيم ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ مِن شَرِّ مَا خَلَقَ وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ وَمِن شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ﴾،بسم الله الرحمن الرحيم ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ مَلِكِ النَّاسِ إِلَهِ النَّاسِ مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ مِنَ الْجِنَّةِ وَ النَّاسِ﴾ بَعْدَ كُلِّ صَلاَةٍ.
Ya kamata a karanta surori uku masu zuwa sau ɗaya bayan sallolin Azahar, La’asar da Isha’i, kuma sau uku bayan sallolin Asuba da Magariba.[Suratul Ikhlas (112)] [Suratul Falaq (113)] [Suratun Nas (114)]
﴿اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لاَ تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلاَ نَوْمٌ لَّهُ مَا فِي السَّمَوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلاَّ بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلاَّ بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضَ وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ﴾ عَقِبَ كلِّ صَلاَةٍ.
Haka kuma yana daga Sunna a karanta Ayatul Kursiyyi bayan kowace salla:[Suratul Baqara, aya ta 255]
((لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ يُحْيِي وَيُمِيتُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ)) عَشْرَ مَرّاتٍ بَعْدَ صَلاةِ الْمَغْرِبِ وَالصُّبْحِ.
(Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne kuma godiya tasa ce, Yana rayarwa kuma Yana kashewa, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan komai.(sau goma bayan sallolin Magariba da Asuba))
((اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ عِلْماً نافِعاً، وَرِزْقاً طَيِّباً، وَعَمَلاً مُتَقَبَّلاً)) بَعْدَ السّلامِ مِنْ صَلاَةِ الفَجْرِ.
(Ya Allah, ina roƙonka ilimi mai amfani, da arziki mai kyau, da ayyuka karɓaɓɓu.)(A faɗi shi bayan sallama a sallar Asuba)