Kalmomin zikiri na safiya da yamma
أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيطَانِ الرَّجِيمِ ﴿اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لاَ تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلاَ نَوْمٌ لَّهُ مَا فِي السَّمَوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلاَّ بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلاَّ بِمَا شَاء وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضَ وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ﴾.
Allah – babu abin bauta da gaskiya sai Shi, Rayayye, Tsayayye da kansa kuma Mai tsayar da kome. Gyangyaɗi ba ya kama Shi, balle barci. Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa nasa ne. Wane ne wanda yake iya yin ceto a wurinsa sai da izininsa? Yana sane da abin da yake gabansu [a yanzu] da abin da zai kasance bayansu, kuma ba sa kewaye da wani abu daga iliminsa sai abin da Ya so. Kujerarsa (Kursiyyi) ta yalwaci sammai da ƙasa, kuma kiyaye su ba ya nauyaya masa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.
(بسم الله الرحمن الرحيم ﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ اللَّهُ الصَّمَدُ لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ وَلَمْ يَكُن لَّهُ كُفُواً أَحَدٌ﴾.) (بسم الله الرحمن الرحيم ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ مِن شَرِّ مَا خَلَقَ وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ وَمِن شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ﴾.) (بسم الله الرحمن الرحيم ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ مَلِكِ النَّاسِ إِلَهِ النَّاسِ مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ مِنَ الْجِنَّةِ وَ النَّاسِ﴾)
([Suratul Ikhlas (112)]( 1 ) Ka ce, Shi Allah Ɗaya ne,( 2 ) Allah Makaɗaici, Wanda ake nufa da bukatu.( 3 ) Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba,( 4 ) Kuma babu wani da yake kamarsa.)([Suratul Falaq (113)] ( 1 ) Ka ce, Ina neman tsari da Ubangijin ketowar asuba( 2 ) Daga sharrin abin da Ya halitta( 3 ) Kuma daga sharrin dare idan ya shiga( 4 ) Kuma daga sharrin masu busa a cikin kulle-kulle( 5 ) Kuma daga sharrin mai hassada idan ya yi hassada. )([Suratun Nas (114)])( 1 ) Ka ce, Ina neman tsari da Ubangijin mutane,( 2 ) Sarkin mutane,( 3 ) Abin bautawar mutane,( 4 ) Daga sharrin mai ɗar-ɗar, mai ɓoyewa -( 5 ) Wanda yake yin ɗar-ɗar a cikin zukatan mutane -( 6 ) Daga aljannu da mutane.
((أَصْبَحْنَا وَأَصْبَحَ الْمُلْكُ لِلَّهِ ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، لاَ إِلَهَ إلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، رَبِّ أَسْأَلُكَ خَيْرَ مَا فِي هَذَا الْيَوْمِ وَخَيرَ مَا بَعْدَهُ ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِي هَذَا الْيَوْمِ وَشَرِّ مَا بَعْدَهُ، رَبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْكَسَلِ وَسُوءِ الْكِبَرِ، رَبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابٍ فِي النَّارِ وَعَذَابٍ فِي الْقَبْرِ)). [ وإذا أمسى قال: أمسينا وأمسى الملك للَّه] [وإذا أمسى قال: رب أسألك خير ما في هذه الليلة، وخير ما بعدها، وأعوذ بك من شر ما في هذه الليلة، وشر ما بعدها.]
‘Mun wayi gari kuma a wannan lokaci mulki duka na Allah ne, kuma godiya ta tabbata ga Allah. Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne kuma godiya tasa ce, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan komai. Ya Ubangijina, ina roƙonka alherin wannan rana da alherin abin da yake biye da ita, kuma ina neman tsarinka daga sharrin wannan rana da sharrin abin da yake biye da ita. Ya Ubangijina, ina neman tsarinka daga kasala da tsufan wauta. Ya Ubangijina, ina neman tsarinka daga azaba a cikin Wuta da azaba a cikin kabari.’
((اللَّهُمَّ بِكَ أَصْبَحْنَا، وَبِكَ أَمْسَيْنَا ، وَبِكَ نَحْيَا، وَبِكَ نَمُوتُ وَإِلَيْكَ النُّشُورُ)). [وإذا أمسى قال: اللَّهم بك أمسينا، وبك أصبحنا، وبك نحيا، وبك نموت، وإليك المصير.]
(Ya Allah, da izininka muka wayi gari kuma da izininka muka yi maraice, da izininka muke rayuwa kuma muke mutuwa kuma gare Ka tashin matattu yake.)[Da maraice:](Ya Allah, da izininka muka yi maraice kuma da izininka muka wayi gari, da izininka muke rayuwa kuma muke mutuwa kuma gare Ka komawarmu take.)
((اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَا إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ بِذَنْبِي فَاغْفِرْ لِي فَإِنَّهُ لاَ يَغْفِرُ الذُّنوبَ إِلاَّ أَنْتَ)).
(Ya Allah, Kai ne Ubangijina, babu abin bauta da gaskiya sai Kai, Kai ne Ka halicce ni kuma ni bawanka ne, kuma ina kan alƙawarinka da wa’adinka gwargwadon iyawata, ina neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata. Ina amincewa da ni’imarka a kaina kuma ina amincewa da zunubina, don haka Ka gafarta mini, domin lallai babu mai gafarta zunubi sai Kai.)
((اللَّهُمَّ إِنِّي أَصْبَحْتُ أُشْهِدُكَ، وَأُشْهِدُ حَمَلَةَ عَرْشِكَ، وَمَلاَئِكَتِكَ، وَجَمِيعَ خَلْقِكَ، أَنَّكَ أَنْتَ اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ وَحْدَكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ، وَأَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُكَ وَرَسُولُكَ)) (أربعَ مَرَّاتٍ).[ وإذا أمسى قال: اللَّهم إني أمسيت...]
(Ya Allah, lallai na wayi gari ina kiran Ka, da masu ɗauke da Al-ʻarshinka, da mala’ikunka, da dukkan halittarka, su zama shaidu cewa Kai ne Allah, babu abin bauta da gaskiya sai Kai, kai kaɗai, ba ka da abokin tarayya, kuma cewa Muhammad bawanka ne kuma Manzonka.) (sau huɗu da safe da maraice)(Lura: da maraice, ana karanta (amsaytu) maimakon (asbahtu).)
((اللَّهُمَّ مَا أَصْبَحَ بِي مِنْ نِعْمَةٍ أَوْ بِأَحَدٍ مِنْ خَلْقِكَ فَمِنْكَ وَحْدَكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ، فَلَكَ الْحَمْدُ وَلَكَ الشُّكْرُ)). [وإذا أمسى قال: اللَّهم ما أمسى بي...]
(Ya Allah, duk wata ni’ima da ni ko wata halittarka muka tashi a kanta, daga gare Ka kaɗai take, ba ka da abokin tarayya, don haka gare Ka ne dukkan godiya take kuma gare Ka ne dukkan shukuru.)(…duk wanda ya faɗi wannan da safe to lallai ya sauke shukurin ranarsa, kuma duk wanda ya faɗe shi da maraice to lallai ya sauke shukurin darensa.)(Lura: da maraice, ana karanta (amsa) maimakon (asbaha).)
((اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَدَنِي، اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي سَمْعِي، اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَصَرِي، لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ. اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْكُفْرِ، وَالفَقْرِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ القَبْرِ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ)) (ثلاثَ مرَّاتٍ).
(Ya Allah, Ka ba jikina lafiya, ya Allah, Ka ba jina lafiya, ya Allah, Ka ba ganina lafiya. Babu abin bauta da gaskiya sai Kai.)(sau uku) (Ya Allah, ina neman tsarinka daga kafirci da talauci, kuma ina neman tsarinka daga azabar kabari. Babu abin bauta da gaskiya sai Kai. (sau uku))
((حَسْبِيَ اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ عَلَيهِ تَوَكَّلتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ)) (سَبْعَ مَرّاتٍ).
Allah ya ishe ni, babu abin bauta da gaskiya sai Shi, gare Shi na dogara kuma Shi ne Ubangijin Al-ʻarshi mai girma.’ (A karanta sau bakwai da Larabci.)
((اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ: فِي دِينِي وَدُنْيَايَ وَأَهْلِي، وَمَالِي، اللَّهُمَّ اسْتُرْ عَوْرَاتِي، وَآمِنْ رَوْعَاتِي، اللَّهُمَّ احْفَظْنِي مِنْ بَينِ يَدَيَّ، وَمِنْ خَلْفِي، وَعَنْ يَمِينِي، وَعَنْ شِمَالِي، وَمِنْ فَوْقِي، وَأَعُوذُ بِعَظَمَتِكَ أَنْ أُغْتَالَ مِنْ تَحْتِي)).
Ya Allah, ina roƙonka afuwa da lafiya a duniya da lahira. Ya Allah, ina roƙonka afuwa da lafiya a cikin al’amurana na addini da na duniya, da iyalina da dukiyata. Ya Allah, Ka rufa mini aibuna kuma Ka kwantar mini da hankali daga firgici. Ya Allah, Ka kiyaye ni daga gaba da baya, da dama da hagu da sama, kuma ina neman tsarinka kada a haɗiye ni daga ƙasa.
((اللَّهُمَّ عَالِمَ الغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَاطِرَ السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضِ، رَبَّ كُلِّ شَيْءٍ وَمَلِيكَهُ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ نَفْسِي، وَمِنْ شَرِّ الشَّيْطانِ وَشَرَكِهِ، وَأَنْ أَقْتَرِفَ عَلَى نَفْسِي سُوءاً، أَوْ أَجُرَّهُ إِلَى مُسْلِمٍ)).
(Ya Allah, Masanin gaibu da abin da ake gani, Mahaliccin sammai da ƙasa, Ubangiji kuma Mamallakin dukkan kome, ina shaida cewa babu abin bauta da gaskiya sai Kai. Ina neman tsarinka daga sharrin raina da sharrin Shaiɗan da shirkarsa, da aikata zalunci a kan raina ko kai shi ga wani Musulmi.)(shirk: haɗa wani da Allah a cikin abubuwan da suka keɓanta da Shi. Wannan na iya faruwa (1) a cikin ɗabi’a ta imani, misali yin imani cewa wani ba Allah ba yana da ikon amfanarwa ko cutarwa, (2) a cikin magana, misali yin rantsuwa da wani ba Allah ba, da (3) a cikin aiki, misali ruku’u ko sujada ga wani ba Allah ba.)
((بِسْمِ اللَّهِ الَّذِي لاَ يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الْأَرْضِ وَلاَ فِي السّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ)) (ثلاثَ مرَّاتٍ).
(Da sunan Allah wanda da sunansa babu abin da yake cutarwa a ƙasa ko a sama kuma Shi ne Mai ji, Mai sani.’(sau uku))
((رَضِيتُ بِاللَّهِ رَبَّاً، وَبِالْإِسْلاَمِ دِيناً، وَبِمُحَمَّدٍ صلى الله عليه وسلم نَبِيّاً)) (ثلاثَ مرَّاتٍ).
(Na yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin addini, da Muhammad a matsayin Annabi.’(sau uku))
((يَا حَيُّ يَا قَيُّومُ بِرَحْمَتِكَ أَسْتَغيثُ أَصْلِحْ لِي شَأْنِيَ كُلَّهُ وَلاَ تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ عَيْنٍ)).
(Ya Rayayye, ya Tsayayye da kansa kuma Mai tsayar da kome, da rahamarka nake neman taimako, Ka gyara mini dukkan al’amurana kuma kada Ka bar ni da kaina, ko da kiftawar ido.)
((أَصْبَحْنَا وَأَصْبَحَ الْمُلْكُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ، اللَّهُـمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَ هَذَا الْيَوْمِ:فَتْحَهُ، وَنَصْرَهُ، وَنورَهُ، وَبَرَكَتَهُ، وَهُدَاهُ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِيهِ وَشَرِّ مَا بَعْدَهُ)). [وإذا أمسى قال: أمسينا وأمسى الملك للَّه ربّ العالمين اللَّهم إني أسألك خير هذه الليلة: فتحها، ونصرها، ونورها، وبركتها، وهداها، وأعوذ بك من شر ما فيها، وشر ما بعدها.]
(Mun wayi gari kuma a wannan lokaci mulki duka na Allah ne, Ubangijin talikai. Ya Allah, ina roƙonka alherin wannan rana, nasarorinta da galabarta, hasken ta da albarkarta da shiriyarta, kuma ina neman tsarinka daga sharrin wannan rana da sharrin abin da yake biye da ita.)[Da maraice, ana karanta addu’ar kamar haka:](Mun yi maraice kuma a wannan lokaci mulki duka na Allah ne, Ubangijin talikai. Ya Allah, ina roƙonka alherin wannan dare, nasarorinsa da galabarsa, hasken sa da albarkarsa da shiriyarsa, kuma ina neman tsarinka daga sharrin wannan dare da sharrin abin da yake biye da shi.)
((أَصْبَحْنا عَلَى فِطْرَةِ الْإِسْلاَمِ، وَعَلَى كَلِمَةِ الْإِخْلاَصِ، وَعَلَى دِينِ نَبِيِّنَا مُحَمَّدٍ صلى الله عليه وسلم، وَعَلَى مِلَّةِ أَبِينَا إِبْرَاهِيمَ، حَنِيفاً مُسْلِماً وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشرِكِينَ)). [وإذا أمسى قال: أمسينا على فطرة الإسلام...]
(Mun tashi a kan fitirar Musulunci, da kalmar imani tsantsa, kuma a kan addinin Annabinmu Muhammad da addinin kakanmu Ibrahim, wanda ya kasance Musulmi kuma mai tsantsar imani, kuma bai kasance daga cikin masu yin shirka ba.)(fitra: addinin Musulunci, tafarkin Ibrahim u.)(Lura: da maraice, ana karanta amsayna maimakon asbahna.)
((سُبْحَانَ اللَّهِ وَبِحَمْدِهِ)) (مائة مرَّةٍ).
(Tsarki ya tabbata ga Allah kuma da godiyarsa.)(sau ɗari)
((لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ)) (عشرَ مرَّات) ، أَوْ (مرَّةً واحدةً عندَ الكَسَلِ).
(Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne kuma godiya tasa ce, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan komai.)( [sau goma ko sau ɗaya idan ana kasala])
((لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ)) (مائةَ مرَّةٍ إذا أصبحَ).
(Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne kuma godiya tasa ce, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan komai.)((sau ɗari a kowace rana))
((سُبْحَانَ اللَّهِ وَبِحَمْدِهِ: عَدَدَ خَلْقِهِ، وَرِضَا نَفْسِهِ، وَزِنَةَ عَرْشِهِ، وَمِدَادَ كَلِمَاتِهِ)) (ثلاثَ مرَّاتٍ إذا أصبحَ).
(Tsarki ya tabbata ga Allah kuma da godiyarsa, gwargwadon adadin halittarsa da yardarsa, da nauyin Al-ʻarshinsa, da tawadar kalmominsa.)(sau uku)
((اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ عِلْماً نَافِعاً، وَرِزْقاً طَيِّباً، وَعَمَلاً مُتَقَبَّلاً)) (إذا أصبحَ).
(Ya Allah, ina roƙonka ilimi mai amfani, da arziki mai kyau, da ayyuka karɓaɓɓu.)
((أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ وَأَتُوبُ إِلَيْهِ)) (مِائَةَ مَرَّةٍ فِي الْيَوْمِ).
‘Ina neman gafarar Allah kuma ina tuba zuwa gare Shi.’ [sau ɗari a rana]
((أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ)) (ثلاثَ مرَّاتٍ إذا أمسى).
(Ina neman tsari da cikakkun kalmomin Allah daga sharrin abin da Ya halitta.)(sau uku da maraice)
((اللَّهُمَّ صَلِّ وَسَلِّمْ عَلَى نَبَيِّنَا مُحَمَّدٍ)) (عشرَ مرَّاتٍ).
‘Ya Allah, Ka yi salati da aminci ga Annabinmu Muhammad.’ [sau goma]