Falalar Zikiri: SubhanAllah, Alhamdulillah da Kabbara

Azkar 12

Ci gaba

Falalar tuna Allah

1 Maimaita ×100

قَالَ صلى الله عليه وسلم مَنْ قَالَ: سُبْحَانَ اللَّهِ وَبِحَمْدِهِ فِي يَوْمٍ مِائَةَ مَرَّةٍ حُطَّتْ خَطَايَاهُ وَلَوْ كَانَتْ مِثْلَ زَبَدِ الْبَحْر)).

(Duk wanda ya ce:(Tsarki ya tabbata ga Allah kuma da godiyarsa.) sau ɗari a cikin yini, ana shafe zunubansa, ko da sun kai kumfar teku.)

2 Maimaita ×10

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((مَنْ قَالَ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ عَشْرَ مِرَارٍ، كَانَ كَمَنْ أَعْتَقَ أَرْبَعَةَ أَنْفُسٍ مِنْ وَلَدِ إِسْمَاعِيلَ)).

(Abu Hurairah ya ruwaito cewa Manzon Allah ya ce: ‘Duk wanda ya ce: (Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya. Mulki nasa ne kuma godiya tasa ce, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan komai.) sau ɗari a cikin yini, yana da ladan ’yanta bayi goma, ana rubuta masa kyawawan ayyuka ɗari, kuma ana shafe masa munanan ayyuka ɗari, kuma yana samun tsari daga Shaiɗan a ranar har maraice, kuma babu wanda zai zo da abin da ya fi shi sai wanda ya yi fiye da haka.)

3 Karanta sau ɗaya

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((كَلِمَتَانِ خَفِيفَتَانِ عَلَى اللِّسَانِ، ثَقِيلَتَانِ فِي الْمِيزَانِ، حَبِيبَتَانِ إِلَى الرَّحْمَنِ: سُبْحَانَ اللَّهِ وَبِحَمْدِهِ، سُبْحانَ اللَّهِ الْعَظِيمِ)).

(Abu Hurairah ya ruwaito cewa Manzon Allah ya ce:’(Akwai) kalmomi biyu, (waɗanda suke) masu sauƙi a kan harshe, masu nauyi a Sikeli kuma masoyan Mai Rahama ne: (Tsarki ya tabbata ga Allah kuma da godiyarsa. Tsarki ya tabbata ga Allah, Mai girma.))

4 Karanta sau ɗaya

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((لَأَنْ أَقُولَ سُبْحَانَ اللَّهِ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَاللَّهُ أَكْبَرُ، أَحَبُّ إِلَيَّ مِمَّا طَلَعَتْ عَلَيْهِ الشَّمسُ)).

(Abu Hurairah ya ruwaito cewa Manzon Allah ya ce: ‘Faɗin: (Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah. Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma Allah ne Mafi girma.) ya fi soyuwa a gare ni fiye da duk abin da rana ta ɓullo a kai.)

5 Maimaita ×100

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((أَيَعْجِزُ أَحَدُكُم أَنْ يَكْسِبَ كُلَّ يَوْمٍ أَلْفَ حَسَنَةٍ)) فَسَأَلَهُ سَائِلٌ مِنْ جُلَسَائِهِ كَيْفَ يَكْسِبُ أَحَدُنَا أَلْفَ حَسَنَةٍ؟ قَالَ: ((يُسَبِّحُ مِائَةَ تَسْبِيحَةٍ، فَيُكتَبُ لَهُ أَلْفُ حَسَنَةٍ أَوْ يُحَطُّ عَنْهُ أَلْفُ خَطِيئَةٍ)).

(Sa’ad ya ce: ‘Muna zaune tare da Manzon Allah , sai ya ce: ‘Shin ɗayanku ba zai iya samun kyawawan ayyuka dubu a kowace rana ba?’ Sai wani ya tambaye shi: Yaya mutum zai samu kyawawan ayyuka dubu? Ya amsa: ‘Ya riƙa cewa: (Tsarki ya tabbata ga Allah.) sau ɗari, domin ana rubuta masa kyawawan ayyuka dubu ko kuma a shafe masa munanan ayyuka dubu.)

6 Karanta sau ɗaya

((مَنْ قَالَ: سُبْحَانَ اللَّهِ الْعَظِيمِ وَبِحَمْدِهِ غُرِسَتْ لَهُ نَخْلَةٌ فِي الْجَنَّةِ)).

(Jabir ya ruwaito cewa Annabi ya ce: ‘Duk wanda ya ce: (Tsarki ya tabbata ga Allah . Mai girma, kuma da godiyarsa.) ana dasa masa itacen dabino a Aljanna.)

7 Karanta sau ɗaya

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((يَا عَبْدَ اللَّهِ بْنَ قَيْسٍ أَلاَ أَدُلُّكَ عَلَى كَنْزٍ مِنْ كُنُوزِ الْجَنَّةِ))؟ فَقُلْتُ: بَلَى يَا رَسُولَ اللَّهِ، قَالَ: ((قُلْ لاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ)).

(Abdullahi ɗan Qais ya ruwaito cewa Annabi ya ce masa: ‘ Ya Abdullahi ɗan Qais, shin ba zan sanar da kai wani taska daga taskokin Aljanna ba?’ Sai ya ce: ‘Ka ce: (Babu dabara babu ƙarfi sai da Allah.))

8 Karanta sau ɗaya

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((أَحَبُّ الْكَلاَمِ إِلَى اللَّهِ أَرْبَعٌ: سُبْحَانَ اللَّهِ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَاللَّهُ أَكْبَرُ، لاَ يَضُرُّكَ بِأَيِّهِنَّ بَدَأتَ)).

(kalmomi mafi soyuwa ga Allah guda huɗu ne: (Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah. Babu abin bauta da gaskiya sai Allah kuma Allah ne Mafi girma.))(ba komai wacce ka fara da ita a cikinsu.)

9 Karanta sau ɗaya

جَاءَ أَعْرَابِيٌّ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم فَقَالَ: عَلِّمْنِي كَلاماً أَقُولُهُ: قَالَ: ((قُلْ: لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، اللَّهُ أَكْبَرُ كَبِيراً، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ كَثِيراً، سُبْحَانَ اللَّهِ رَبِّ العَالَمِينَ، لاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ)) قَالَ: فَهَؤُلاَءِ لِرَبِّي، فَمَا لِي؟ قَالَ: ((قُلْ: اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي، وَارْحَمْنِي، وَاهْدِنِي، وَارْزُقْنِي)).

(Sa’ad ɗan Abi Waqqas ya ruwaito cewa wani mutum ya zo wurin Manzon Allah ya ce masa: ‘Koya mini wani abu da zan riƙa faɗa?’ Ya ce: ‘Ka ce: (Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya. Allah ne Mafi girma kuma godiya mai yawa ta tabbata ga Allah. Tsarki ya tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Babu dabara babu ƙarfi sai da Allah, Mabuwayi, Mai hikima.) Sai mutumin ya ce: ‘Waɗannan na Ubangijina ne, to menene nawa?’ Ya amsa: ‘Ka ce:(Ya Allah, Ka gafarta mini, Ka yi mini rahama, Ka shiryar da ni kuma Ka azurta ni.))

10 Karanta sau ɗaya

كَانَ الرَّجُلُ إِذَا أَسْلَمَ عَلَّمَهُ النَّبيُّ صلى الله عليه وسلم الصَّلاَةَ ثُمَّ أَمَرَهُ أَنْ يَدْعُوَ بِهَؤُلاَءِ الْكَلِمَاتِ: ((اللَّهُمَّ اغْفِرِ لِي، وَارْحَمْنِي، وَاهْدِنِي، وَعَافِنِي وَارْزُقْنِي)).

(Tariq Al-Ashja’i ya ce: ‘Idan wani ya shiga Musulunci, Annabi yakan koya masa yadda ake salla sannan ya umarce shi da yin addu’a da waɗannan kalmomi: (Ya Allah, Ka gafarta mini, Ka yi mini rahama, Ka shiryar da ni, Ka ba ni lafiya kuma Ka azurta ni.))

11 Karanta sau ɗaya

((إِنَّ أَفْضَلَ الدُّعَاءِ الْحَمْدُ لِلَّهِ، وَأَفْضَلَ الذِّكْرِ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ)).

(Jabir ɗan Abdullah ya ruwaito cewa Manzon Allah ya ce: ‘Lallai, mafi kyawun addu’a ita ce: (Godiya ta tabbata ga Allah.) kuma lallai, mafi kyawun zikiri shi ne: (Babu abin bauta da gaskiya sai Allah.))

12 Karanta sau ɗaya

الباقيات الصالحات : سبحان الله والحمد لله ، ولا إله إلا الله ،والله أكبر ،و لا حول ولا قوة إلا بالله

Ayyuka nagari masu dawwama su ne ‘Tsarki ya tabbata ga Allah’, da ‘Godiya ta tabbata ga Allah’, da ‘Babu abin bauta sai Allah’, da ‘Allah ne Mafi girma’, da ‘Babu dabara babu ƙarfi sai da Allah’

Masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni: kalmomin zikiri masu sauƙi da ladansu.

Tushe: Hisn al-Muslim (Sansanin Musulmi). Rubutun Larabci tare da fassara.

Tambayoyi

Daga ina azkar na "Falalar Zikiri: SubhanAllah, Alhamdulillah da Kabbara" suka fito?

An ɗauko su ne daga Hisn al-Muslim, tarin azkar da addu'o'i daga Alƙur'ani da ingantacciyar Sunna.

Sau nawa ya kamata a maimaita kowane zikiri?

Ana nuna lambar a saman kowane zikiri. Inda babu lamba, ana faɗa sau ɗaya.

This page is translated with machine assistance and may contain mistakes. The English and Arabic versions are our reference. About our sources