Abin da za a faɗa kafin kwanciya
((يَجْمَعُ كَفَّيْهِ ثُمَّ يَنْفُثُ فِيهِمَا فَيَقْرَأُ فِيهِمَا:بسم الله الرحمن الرحيم ﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ اللَّهُ الصَّمَدُ لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ وَلَمْ يَكُن لَّهُ كُفُواً أَحَدٌ﴾. بسم الله الرحمن الرحيم ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ مِن شَرِّ مَا خَلَقَ وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ وَمِن شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ﴾. بسم الله الرحمن الرحيم ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ مَلِكِ النَّاسِ إِلَهِ النَّاسِ مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ مِنَ الْجِنَّةِ وَ النَّاسِ﴾ ثُمَّ يَمْسَحُ بِهِمَا مَا اسْتَطَاعَ مِنْ جَسَدِهِ يَبْدَأُ بِهِمَا عَلَى رَأْسِهِ وَوَجْهِهِ وَمَا أَقبَلَ مِنْ جَسَدِهِ)) (يفعلُ ذلك ثلاثَ مرَّاتٍ).
(Duk lokacin da Annabi ya kwanta a gadonsa kowane dare, yakan haɗa tafukan hannayensa, ya yi tofi (wani irin tofi ne wanda mafi yawansa iska ne da ɗan miyau kaɗan) a cikinsu, ya karanta surori uku na ƙarshe na Alƙur’ani (Al-Ikhlas, Al-Falaq, An-Nas) sannan ya shafa dukkan jikinsa gwargwadon iyawa da hannayensa, yana farawa da kansa da fuskarsa sannan sauran sassan jiki, yakan yi haka sau uku.)
﴿اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لاَ تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلاَ نَوْمٌ لَّهُ مَا فِي السَّمَوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْـــــــــــدَهُ إِلاَّ بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلاَّ بِمَا شَاء وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضَ وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ﴾.
Allah – babu abin bauta da gaskiya sai Shi, Rayayye, Tsayayye da kansa kuma Mai tsayar da kome. Gyangyaɗi ba ya kama Shi, balle barci. Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa nasa ne. Wane ne wanda yake iya yin ceto a wurinsa sai da izininsa? Yana sane da abin da yake gabansu [a yanzu] da abin da zai kasance bayansu, kuma ba sa kewaye da wani abu daga iliminsa sai abin da Ya so. Kujerarsa (Kursiyyi) ta yalwaci sammai da ƙasa, kuma kiyaye su ba ya nauyaya masa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.
﴿آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مِن رَّبِّهِ وَالْمُؤْمِنُونَ كُلٌّ آمَنَ بِاللَّهِ وَمَلآئِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لاَ نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّن رُّسُلِهِ وَقَالُواْ سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ لاَ يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْساً إِلاَّ وُسْعَهَا لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ رَبَّنَا لاَ تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا رَبَّنَا وَلاَ تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْراً كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِنَا رَبَّنَا وَلاَ تُحَمِّلْنَا مَا لاَ طَاقَةَ لَنَا بِهِ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَآ أَنتَ مَوْلاَنَا فَانصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ﴾.
( 285 ) Manzo ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa, kuma muminai ma. Dukansu sun yi imani da Allah da mala’ikunsa da littattafansa da manzanninsa, [suna cewa], Ba ma bambanta tsakanin kowane ɗaya daga manzanninsa. Kuma suka ce, Mun ji kuma mun yi biyayya. [Muna roƙon] gafararka, ya Ubangijinmu, kuma zuwa gare Ka ne makoma [ta ƙarshe].( 286 ) Allah ba Ya ɗora wa rai sai abin da ya iya. Yana da [sakamakon] abin da ya aikata na [alheri], kuma yana ɗaukar [sakamakon] abin da ya aikata na [sharri]. Ya Ubangijinmu, kada Ka kama mu idan mun manta ko mun yi kuskure. Ya Ubangijinmu, kuma kada Ka ɗora mana nauyi kamar wanda Ka ɗora wa waɗanda suke gabaninmu. Ya Ubangijinmu, kuma kada Ka ɗora mana abin da ba mu da ikon ɗauka. Kuma Ka yi mana afuwa; kuma Ka gafarta mana; kuma Ka ji ƙan mu. Kai ne Majiɓincinmu, don haka Ka ba mu nasara a kan mutane kafirai.
((بِاسْمِكَ رَبِّي وَضَعْتُ جَنْبِي، وَبِكَ أَرْفَعُهُ، فَإِن أَمْسَكْتَ نَفْسِي فارْحَمْهَا، وَإِنْ أَرْسَلْتَهَا فَاحْفَظْهَا، بِمَا تَحْفَظُ بِهِ عِبَادَكَ الصَّالِحِينَ)).
(Da sunanka, ya Ubangijina, na kwanta kuma da sunanka zan tashi, to idan Ka riƙi raina sai Ka yi masa rahama, kuma idan Ka mayar da raina sai Ka kiyaye shi kamar yadda Kake kiyaye bayinka salihai.)
((اللَّهُمَّ إِنَّكَ خَلَقْتَ نَفْسِي وَأَنْتَ تَوَفَّاهَا، لَكَ مَمَاتُهَا وَمَحْياهَا، إِنْ أَحْيَيْتَهَا فَاحْفَظْهَا، وَإِنْ أَمَتَّهَا فَاغْفِرْ لَهَا. اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ العَافِيَةَ)).
(Ya Allah, lallai Kai ne Ka halicci raina kuma Kai ne za Ka karɓi ransa, a gare Ka rayuwarsa da mutuwarsa suke. Idan Ka bar raina da rai to Ka kiyaye shi, kuma idan Ka karɓi ransa to Ka gafarta masa. Ya Allah, ina roƙonka lafiya.)
((اللَّهُمَّ قِنِي عَذَابَكَ يَوْمَ تَبْعَثُ عِبَادَكَ)).
(Ya Allah, Ka tsare ni daga azabarka a ranar da ake tayar da bayinka.)
((بِاسْمِكَ اللَّهُمَّ أَمُوتُ وَأَحْيَا)).
(Da sunanka, ya Allah, nake rayuwa kuma nake mutuwa.)
((سُبْحَانَ اللَّهِ (ثلاثاً وثلاثين) وَالْحَمْدُ لِلَّهِ (ثلاثاً وثلاثين) وَاللَّهُ أَكْبَرُ (أربعاً وثلاثينَ))).
(Tsarki ya tabbata ga Allah. (sau talatin da uku) Godiya ta tabbata ga Allah.(sau talatin da uku) Allah ne Mafi girma.(sau talatin da huɗu))
((اللَّهُمَّ رَبَّ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ وَرَبَّ الأَرْضِ، وَرَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، رَبَّنَا وَرَبَّ كُلِّ شَيْءٍ، فَالِقَ الْحَبِّ وَالنَّوَى، وَمُنْزِلَ التَّوْرَاةِ وَالْإِنْجِيلِ، وَالْفُرْقَانِ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ كُلِّ شَيْءٍ أَنْتَ آخِذٌ بِنَاصِيَتِهِ. اللَّهُمَّ أَنْتَ الأَوَّلُ فَلَيْسَ قَبْلَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ الآخِرُ فَلَيسَ بَعْدَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ الظَّاهِرُ فَلَيْسَ فَوْقَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ الْبَاطِنُ فَلَيْسَ دُونَكَ شَيْءٌ، اقْضِ عَنَّا الدَّيْنَ وَأَغْنِنَا مِنَ الْفَقْرِ)).
(Ya Allah, Ubangijin sammai bakwai da Al-ʻarshi mai girma, Ubangijinmu kuma Ubangijin dukkan kome, Mai tsattsagar ƙwaya da ƙwallon dabino, Mai saukar da Attaura, da Injila da Furqan, ina neman tsarinka daga sharrin dukkan abin da Kake riƙe da tuƙewarsa (wato Kana da cikakken iko a kansa). Ya Allah, Kai ne na Farko, don haka babu wani abu kafin Kai, kuma Kai ne na Ƙarshe, don haka babu wani abu bayan Kai.Kai ne Az-Zahir, don haka babu wani abu sama da Kai, kuma Kai ne Al-Batin, don haka babu wani abu da ya fi Kai kusanci.Ka biya mana bashinmu kuma Ka wadatar da mu daga talauci.)(Attaura: Littafin da aka saukar wa Musa u.)(Injila: Littafin da aka saukar wa Isa u.)(Furqan: Ɗaya daga cikin sunayen Alƙur’ani masu yawa, ma’ana: Mai rarrabewa tsakanin gaskiya da ƙarya.)(Az-Zahir: Yana nuna girman siffofinsa da ƙanƙantar kowace halitta idan aka kwatanta da girmansa da ɗaukakarsa, domin Yana sama da dukkan halittarsa a zatinsa da siffofinsa.)(Al-Batin: Yana nuna saninsa da iliminsa na dukkan asirai, na abin da yake cikin zukata da mafi zurfin abubuwa, kamar yadda yake nuna kusancinsa da kowa, kusanci da ya dace da girmansa.)
((الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَطْعَمَنَا وَسَقَانَا، وَكَفَانَا، وَآوَانَا، فَكَمْ مِمَّنْ لاَ كَافِيَ لَهُ وَلاَ مُؤْوِيَ)).
(Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya ciyar da mu kuma Ya shayar da mu, kuma Ya wadatar da mu kuma Ya ba mu mafaka, domin kuwa da yawa ne waɗanda ba su da wanda zai wadatar da su ko ya ba su mafaka.)
((اللَّهُمَّ عَالِمَ الغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَاطِرَ السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضِ، رَبَّ كُلِّ شَيْءٍ وَمَلِيكَهُ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ نَفْسِي، وَمِنْ شَرِّ الشَّيْطانِ وَشِرْكِهِ، وَأَنْ أَقْتَرِفَ عَلَى نَفْسِي سُوءاً، أَوْ أَجُرَّهُ إِلَى مُسْلِمٍ)).
(Ya Allah, Masanin gaibu da abin da ake gani, Mahaliccin sammai da ƙasa, Ubangiji kuma Mamallakin dukkan kome, ina shaida cewa babu abin bauta da gaskiya sai Kai. Ina neman tsarinka daga sharrin raina da sharrin Shaiɗan da shirkarsa, da aikata zalunci a kan raina ko kai shi ga wani Musulmi.)(shirk: haɗa wani da Allah a cikin abubuwan da suka keɓanta da Shi. Wannan na iya faruwa (1) a cikin ɗabi’a ta imani, misali yin imani cewa wani ba Allah ba yana da ikon amfanarwa ko cutarwa, (2) a cikin magana, misali yin rantsuwa da wani ba Allah ba, da (3) a cikin aiki, misali ruku’u ko sujada ga wani ba Allah ba.)
((يَقْرَأُ ﴿الم﴾ تَنْزِيلَ السَّجْدَة ِ، وَتَبَارَكَ الَّذي بِيَدِهِ الْمُلْكُ)).
(Annabi bai kasance yana barci ba sai ya karanta Suratus-Sajda (sura ta 32) da Suratul Mulk (sura ta 67).)
((اللَّهُمَّ أَسْلَمْتُ نَفْسِي إِلَيْكَ، وَفَوَّضْتُ أَمْرِي إِلَيْكَ، وَوَجَّهْتُ وَجْهِي إِلَيْكَ، وَأَلْجَأْتُ ظَهْرِي إِلَيْكَ، رَغْبَةً وَرَهْبَةً إِلَيْكَ، لاَ مَلْجَأَ وَلاَ مَنْجَا مِنْكَ إِلاَّ إِلَيْكَ، آمَنْتُ بِكِتَابِكَ الَّذِي أَنْزَلْتَ، وَبِنَبِيِّكَ الَّذِي أَرْسَلْتَ)).
(Ya Allah, na miƙa raina gare Ka, kuma na ba da al’amarina gare Ka, kuma na juyar da fuskata zuwa gare Ka, kuma na dogara gare Ka gaba ɗaya, cikin fata da tsoronka.Lallai babu mafaka babu kuma wurin tsira daga Gare Ka sai zuwa gare Ka. Na yi imani da Littafinka da Ka saukar da Annabinka da Ka aiko.)(Idan ka mutu, to za ka mutu a kan fitra.)(fitra: addinin Musulunci, tafarkin Ibrahim u.)
Addu'o'in tashi daga barci
(.الْحَمْدُ للَّهِ الَّذِي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا، وَإِلَيْهِ النُّشُورُ )
(Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya raya mu bayan Ya karɓi ranmu, kuma gare Shi tashin matattu yake.)
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَريكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، سُبْحَانَ اللَّهِ، وَالْحَمْدُ للَّهِ، وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَاللَّهُ أَكبَرُ، وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ الْعَلِيِّ الْعَظِيمِ، رَبِّ اغْفرْ لِي
(Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, mulki da godiya nasa ne kuma Shi Mai cikakken iko ne a kan komai. Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma godiya ta tabbata ga Allah, kuma babu abin bauta da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma kuma babu dabara babu ƙarfi sai da Allah, Maɗaukaki, Mai girma.Ya Ubangijina Ka gafarta mini)
( الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي عَافَانِي فِي جَسَدِي، وَرَدَّ عَلَيَّ رُوحِي، وَأَذِنَ لي بِذِكْرِهِ )
(Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya dawo mini da lafiyata kuma Ya mayar mini da raina kuma Ya yarje mini in ambace Shi.)
﴿ إِنَّ فِي خَلْقِ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ وَاخْتِلاَفِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ لَآيَاتٍ لأُوْلِي الألْبَابِ الَّذِينَ يَذْكُرُونَ اللَّهَ قِيَاماً وَقُعُوداً وَعَلَىَ جُنُوبِهِمْ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلْقِ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ رَبَّنَا مَا خَلَقْتَ هَذا بَاطِلاً سُبْحَانَكَ فَقِنَا عَذَابَ النَّارِ رَبَّنَا إِنَّكَ مَن تُدْخِلِ النَّارَ فَقَدْ أَخْزَيْتَهُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ رَّبَّنَا إِنَّنَا سَمِعْنَا مُنَادِياً يُنَادِي لِلإِيمَانِ أَنْ آمِنُواْ بِرَبِّكُمْ فَآمَنَّا رَبَّنَا فَاغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرْ عَنَّا سَيِّئَاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ الأبْرَارِ رَبَّنَا وَآتِنَا مَا وَعَدتَّنَا عَلَى رُسُلِكَ وَلاَ تُخْزِنَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ إِنَّكَ لاَ تُخْلِفُ الْمِيعَادَ فَاسْتَجَابَ لَهُمْ رَبُّهُمْ أَنِّي لاَ أُضِيعُ عَمَلَ عَامِلٍ مِّنكُم مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَى بَعْضُكُم مِّن بَعْضٍ فَالَّذِينَ هَاجَرُواْ وَأُخْرِجُواْ مِن دِيَارِهِمْ وَأُوذُواْ فِي سَبِيلِي وَقَاتَلُواْ وَقُتِلُواْ لأُكَفِّرَنَّ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَلأُدْخِلَنَّهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ ثَوَاباً مِّن عِندِ اللَّهِ وَاللَّهُ عِندَهُ حُسْنُ الثَّوَابِ لاَ يَغُرَّنَّكَ تَقَلُّبُ الَّذِينَ كَفَرُواْ فِي الْبِلاَدِ مَتَاعٌ قَلِيلٌ ثُمَّ مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ وَبِئْسَ الْمِهَادُ لَكِنِ الَّذِينَ اتَّقَوْاْ رَبَّهُمْ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا نُزُلاً مِّنْ عِندِ اللَّهِ وَمَا عِندَ اللَّهِ خَيْرٌ لِّلأَبْرَارِ وَإِنَّ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ لَمَن يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْكُمْ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيْهِمْ خَاشِعِينَ لِلَّهِ لاَ يَشْتَرُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ ثَمَناً قَلِيلاً أُوْلَئِكَ لَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ إِنَّ اللَّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ اصْبِرُواْ وَصَابِرُواْ وَرَابِطُواْ وَاتَّقُواْ اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ ﴾
( 190 ) Lallai, a cikin halittar sammai da ƙasa da bambancin dare da yini akwai ayoyi ga masu hankali.( 191 ) Waɗanda suke ambaton Allah a tsaye da a zaune da a kwance a kan ɓangarorinsu, kuma suna tunani a cikin halittar sammai da ƙasa, [suna cewa], Ya Ubangijinmu, Ba Ka halicci wannan a banza ba; tsarki ya tabbata a gare Ka [daga wannan]; to Ka tsare mu daga azabar Wuta.( 192 ) Ya Ubangijinmu, lallai wanda Ka shigar da shi Wuta - to haƙiƙa Ka wulakanta shi, kuma babu masu taimako ga azzalumai.( 193 ) Ya Ubangijinmu, lallai mu mun ji mai kira yana kira zuwa ga imani, [yana cewa], ‘Ku yi imani da Ubangijinku,’ sai muka yi imani. Ya Ubangijinmu, to Ka gafarta mana zunubanmu kuma Ka kawar mana da miyagun ayyukanmu kuma Ka karɓi ranmu tare da salihai.( 194 ) Ya Ubangijinmu, kuma Ka ba mu abin da Ka yi mana alƙawari ta bakin manzanninka kuma kada Ka wulakanta mu a Ranar Ƙiyama. Lallai, Ba Ka saɓa wa alƙawari.( 195 ) Sai Ubangijinsu Ya amsa musu, Ba zan tauye aikin wani mai aiki daga cikinku ba, namiji ne ko mace; sashenku daga sashe ne. To waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajensu kuma aka cutar da su saboda hanyata kuma suka yi yaƙi kuma aka kashe su - lallai zan kawar musu da miyagun ayyukansu, kuma lallai zan shigar da su gidajen Aljanna ƙarƙashinsu koguna suna gudana, lada ne daga Allah, kuma Allah a wurinsa akwai mafi kyawun lada.( 196 ) Kada yawon kafirai [da suke yi ba tare da hanawa ba] a cikin ƙasa ya ruɗe ka.( 197 ) [Wannan] ɗan jin daɗi ne kaɗan; sannan makomarsu [ta ƙarshe] Jahannama ce, kuma mummunan wurin hutawa ne.( 198 ) Amma waɗanda suka ji tsoron Ubangijinsu za su sami gidajen Aljanna ƙarƙashinsu koguna suna gudana, suna dawwama a cikinsu, a matsayin baƙunta daga Allah. Kuma abin da yake wurin Allah shi ne mafi alheri ga salihai.( 199 ) Kuma lallai, daga cikin Ma’abota Littafi akwai waɗanda suke yin imani da Allah da abin da aka saukar muku da abin da aka saukar musu, [suna masu] tawali’u ga Allah. Ba sa musayar ayoyin Allah da ɗan kuɗi kaɗan.Waɗannan suna da ladansu a wurin Ubangijinsu. Lallai, Allah Mai gaggawar hisabi ne.( 200 ) Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi haƙuri kuma ku jure kuma ku tsaya a kan iyaka kuma ku ji tsoron Allah ko ku rabauta.