Abin da za a faɗa idan an ji kiran sallah
يَقُولُ مِثْلَ مَا يَقُولُ المُؤَذِّنُ إِلاَّ فِي ((حَيَّ عَلَى الصَّلَاةِ وَحَيَّ عَلَى الْفَلَاحِ)) فَيقُولُ: ((لاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ)).
‘Ana maimaita abin da mai kiran salla (muʼazzini) yake faɗa, sai dai idan ya ce: Hayya ʻalas-salah (ko) hayya ʻalal-falah ‘ku zo ga salla, ku zo ga cin nasara’, a maimakon haka sai a ce: La hawla wala quwwata illa billah. ‘Babu dabara babu ƙarfi sai da Allah.’
يَقُولُ: ((وَأَنَا أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ وَأَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، رَضِيتُ بِاللَّهِ رَبَّاً، وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولاً، وَبِالْإِسْلاَمِ دِينَاً)) ((يَقُولُ ذَلِكَ عَقِبَ تَشَهُّدِ الْمُؤَذِّنِ)).
Nan da nan bayan shaidar imani da mai kiran salla ya yi, sai a ce:‘Ni ma ina shaida cewa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, kuma cewa Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa. Na yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Muhammad a matsayin Manzo, da Musulunci a matsayin addini.’
((يُصَلِّي عَلَى النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم بَعْدَ فَرَاغِهِ مِنْ إِجَابَةِ الْمُؤَذِّنِ)).
‘Sannan sai a yi salati ga Annabi (sallallahu ʻalaihi wa sallam) bayan an amsa kiran mai kiran salla’.
يَقُولُ: ((اللَّهُمَّ رَبَّ هَذِهِ الدَّعْوَةِ التَّامَّةِ، وَالصَّلاَةِ الْقَائِمَةِ، آتِ مُحَمَّداً الْوَسِيلَةَ وَالْفَضِيلَةَ، وَابْعَثْهُ مَقَامَاً مَحمُوداً الَّذِي وَعَدْتَهُ، [إِنَّكَ لَا تُخْلِفُ الْمِيعَادَ])).
‘Ya Allah, Ma’abucin wannan kira cikakke kuma Ma’abucin wannan salla da za a tsayar, Ka ba Muhammad al-wasila da al-fadila, kuma Ka tashe shi a matsayi abin yabo wanda Ka yi masa alƙawari. Lallai Kai ba ka saɓa alƙawari.’al-wasila: Wani matsayi a Aljanna.al-fadila: Wani matsayi da ya fi na sauran halitta.matsayi abin yabo: Matsayin da dukkan halitta za ta yabe shi a kansa, domin a gaggauta hisabi kuma a huta daga tsawon tsayuwa, ko aikin ceto.
((يَدْعُو لِنَفسِهِ بَيْنَ الْأَذَانِ وَالْإِقَامَةِ فَإِنَّ الدُّعَاءَ حِينَئِذٍ لاَ يُرَدُّ)).
Haka kuma ya kamata mutum ya yi addu’a ga kansa a lokacin da yake tsakanin kiran salla (adhan) da iƙama, domin addu’a a irin wannan lokaci ba a mayar da ita.