Tuba da neman gafara
قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم: ((وَاللَّهِ إِنِّي لأَسْتَغفِرُ اللَّهَ وَأَتُوبُ إِلَيْهِ فِي الْيَوْمِ أَكْثَرَ مِنْ سَبْعِينَ مَرَّةٍ)).
(Manzon Allah ya ce: ‘Wallahi, ina neman gafarar Allah kuma ina tuba zuwa gare Shi, fiye da sau saba’in a rana.)
وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((يَا أَيُّهَا النَّاسُ تُوبُوا إِلَى اللَّهِ فَإِنِّي أَتُوبُ فِي الْيَوْمِ إِلَيْهِ مِائَةَ مَرَّةٍ)).
(Ya kuma ce: ‘Ya ku mutane, ku tuba! Lallai ni ina tuba zuwa ga Allah sau ɗari a rana.)
وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((مَنْ قَالَ أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ الْعَظيمَ الَّذِي لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ القَيّوُمُ وَأَتُوبُ إِلَيهِ، غَفَرَ اللَّهُ لَهُ وَإِنْ كَانَ فَرَّ مِنَ الزَّحْفِ)).
(Ya kuma ce: ‘Duk wanda ya ce:(Ina neman gafarar Allah, wanda babu abin bauta da gaskiya sai Shi, Rayayye, Tsayayye da kansa kuma Mai tsayar da kome, kuma ina tuba zuwa gare Shi.) Allah zai gafarta masa ko da ya kasance wanda ya gudu a lokacin ci gaban runduna.)
وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((أَقْرَبُ مَا يَكُونُ الرَّبُّ مِنَ الْعَبْدِ فِي جَوْفِ اللَّيْلِ الآخِرِ فَإِنِ اسْتَطَعْتَ أَنْ تَكُونَ مِمَّنْ يَذْكُرُ اللَّهَ فِي تِلْكَ السَّاعَةِ فَكُنْ)).
(Ya ce: ‘Mafi kusancin da Ubangiji yake yi ga bawansa shi ne a tsakiyar dare, don haka idan za ka iya kasancewa daga cikin masu ambaton Allah a lokacin, to ka kasance.)
وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((أَقْرَبُ مَا يَكُونُ الْعَبْدُ مِنْ رَبِّهِ وَهُوَ سَاجِدٌ فَأَكثِرُوا الدُّعَاءَ)).
(Ya kuma ce: ‘Mafi kusancin da bawa yake yi ga Ubangijinsa shi ne lokacin da yake sujada, don haka ku yawaita addu’a a cikinta.)
وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((إِنَّهُ لَيُغَانُ عَلَى قَلْبِي وَإِنِّي لأَسْتَغْفِرُ اللَّهَ فِي الْيَوْمِ مِائَةَ مَرَّةٍ)).
(Ya kuma ce: ‘Lallai zuciyata tana shagala, kuma lallai ina neman gafarar Allah sau ɗari a rana.)(shagala: wato a yanayin ‘mantuwa’. Annabi yana ƙara yawan ambaton Ubangijinsa a koyaushe, domin samun kusanci ga Allah da kuma tsoron Allah, har ta kai ga cewa idan wannan ƙarfi ya ragu ko kaɗan, yakan ɗauke shi a matsayin zunubi, sannan ya yi gaggawar neman gafara daga Allah.)