((الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَطْعَمَنِي هَذَا، وَرَزَقَنِيهِ، مِنْ غَيْرِ حَوْلٍ مِنِّي وَلاَ قُوَّةٍ)).
(Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan, kuma Ya azurta ni da shi ba tare da wata dabara ko ƙarfi daga gare ni ba.)
((الْحَمْدُ لِلَّهِ حَمْداً كَثِيراً طَيِّباً مُبَارَكاً فِيهِ، غَيْرَ [مَكْفِيٍّ وَلاَ ] مُوَدَّعٍ، وَلاَ مُسْتَغْنَىً عَنْهُ رَبَّنَا)).
(Godiya ta tabbata ga Allah, godiya mai yawa, mai kyau, mai albarka, wadda ba ta ƙarewa, wadda ba za mu yi bankwana da ita ba, kuma wadda ba za mu rabu da ita ba, Shi ne Ubangijinmu.)(Akwai wasu ra’ayoyi game da fahimtar wannan addu’a, daga cikinsu: Godiya ta tabbata ga Allah, godiya mai yawa, mai kyau, mai albarka. Shi ne Wanda Yake wadatarwa, Yake ciyarwa, ba a ciyar da Shi. Wanda ake begensa tare da abin da yake wurinsa, kuma Wanda ake bukata, Shi ne Ubangijinmu.)